Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta a Kano INEC Ambasada Abdu A, Zango ya jagoranci bayar da shedar cin zabe ga mambobi na majalisar dokokin jiha a ofishin hukumar ta INEC da ke Kano a wannan Alhamis 20.04.2023.
An dai kai ga kammala zaben shugaban kasa da na gwamna da ‘yan majalisa na tarrayya da jiha zaben da za a ce an yi shi lafiya duk da kalubale nan da can, sai dai idan aka kalli halin da jihar ke ciki kawo yanzu sai a ce san barka.
A wannan Alhamis ce dai hukumar zabe mai zaman kanta INEC a jihar ta Kano ta ba da takardun shedar cin zabe ga mambobin majalisar dokokin jiha sha hudu da aka cike gibin zabensu a karshen makon da ya gabata. Wannan mataki ne dai ya kawo karshen duk matakan da aka bi wajan gudanar da zabe a wannan jiha a cewar Ambasada Abdu A. Zango kwamishinan zabe na jihar ta Kano.
“Muna farinciki cewa mun yi wa kowa adalci don jama’a sun nuna godiya da goyon baya an yi an gama lafiya. Ku kanku ‘yan jarida kuna gani ga shinan jihar Kano tana zaune lafiya, saboda an yi adalci, ba don haka ba ku kanku ‘yanjarida sheda ne da sai aga ana ta tarzoma.Ina jan hankali na ‘yansiyasa su yi koyi da wannan. Su yi wa al’umma aiki. An kammala zabe abin da yayi saura shine a yi aiki don inganta lafiyar al’umma da tattalin arzikinsu da dai sauransu.”
A cewar Ambasada Zango hadin kan jami’an tsaro da hukumar INEC ta samu a Kano baya ji a kwai wata jiha da ta samu wannan gata, lamarin da ya taimaka mata matuka wajen gudanar da aikinta.
Haka nan ya ce ba za su manta da shawarwari da masarautar Kano ta basu ba musamman Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ga kuma rawar da kungiyoyin sakai suka taka da kafafan yada labarai.
Da yake nasa tsokaci jim kadan bayan karbar takardar shedar cin zabe dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ungoggo Aminu Sa’ad Ungoggo ya ce babbar godiyarsu ta tabbata ga Allah kuma suna godiya ga jagoran ‘yan Kawankwasiya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf zababben gwamna da shugaban jam’iyyar ta NNPP Umar Haruna Doguwa.
Ya kara da cewa: “A karo na biyu kenan nake wakilatar al’umma ta don haka zan zage damtse don tabbatar da ganin nayi wa al’ummar karamar hukumar Ungoggo wakilci nagari. Da fitar da dokoki masu nagarta ga al’ummar Kano. Haka kuma za mu kulla alaka mai kyau da bangaren zartaswa don tabbatar da ganin an yi wa al’umma ayyuka, za mu kuma bibiyi ayyukan don tabbatar da ganin an masu ayyuka ingantattu.”
A karshe dan majalisar Aminu Saad Ungoggo ya nemi al’ummar jihar Kano su taya ‘yanmajalisar da addu’a ta yadda za su yi aiki mai nagarta da zai daga martabar jihar ta Kano. Ya kuma yaba wa duk masu ruwa da tsaki kan harkokin na zabe musamman hukumar ta INEC kan aikin da ta yi bisa jajircerwa.
Leave a Reply