Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Buhari Ya Dawo Abuja Daga Kasar Saudiyya

0 239

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan ziyarar kwanaki takwas da ya yi a kasar Saudiyya.

 

Shugaban wanda ya sauka a yammacin Larabar da ta gabata a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja ya samu tarba daga shugaban ma’aikatan sa Farfesa Ibrahim Gambari.

 

Shugaban na Najeriya dai ya tafi kasar Saudiyya tun ranar Talata 11 ga watan Afrilu.

 

KU KARANTA KUMA: Ziyarar Saudiyya: Shugaba Buhari ya gana da malaman addini da na gargajiya

Yayin da yake kasar Saudiyya, ya yi karamar aikin hajjin da aka fi sani da Umrah inda ya gana da takwaransa na Jamhuriyar Chadi, Mahamat Deby-Itno.

KU KARANTA KUMA: Ziyarar Saudiyya: Shugaba Buhari ya gudanar da aikin Umrah

 

Shugaba Buhari ya kuma ziyarci Masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam tare da zagayawa a wajen bikin baje kolin tarihin Manzon Allah a birnin Madina inda ya kai kara domin a samu daidaiton fahimtar addinin Musulunci ta hanyar gyara kuskuren da aka yi wa addinin da aka yi shekaru aru-aru.

KU KARANTA KUMA: Ziyarar Saudiyya: Shugaba Buhari ya gana da gwamnoni

 

Ya kuma gana da wasu Gwamnonin Jihohi da malaman addini da sarakunan gargajiya, inda suka tattauna batutuwan da za su dore da hadin kai da kuma kawo ci gaban al’umma.

 

Wannan dai ita ce ziyararsa ta karshe zuwa kasar Saudiyya a matsayin shugaban Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *