Take a fresh look at your lifestyle.

HARIN KUJE BA ZAI MAI MAITA BA-SHUGABA BUHARI

0 380

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci rundunar sojin Najeriya da sauran Jamian tsaro das u dauki kwakwaran matakai na ganin  harin daya auku a babban gidan yarin Kuje bai sake faruwa a koina cikin kasar nan ba.

Shugaban ya bada wannan umurnin ne a taron majalisar Tsaro ta kasa da aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Alhamis.

Ministan kula da harkokin ‘yan sandan Najeriya , Maigari Dingyadi ya sanar da haka ga manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan da kamala taron da Shugaba Buhari ya jagoranta.

Yace: “ a yau da Wannan abunda ya faru Shugaban kasa ya nuna alhinin shi saboda haka ya shirya wannan taro  akan makasudin faruwar wannan harin gidan yari da kuma da Jamian tsaro,domin tattaunawa dasu har ma ya nemi suyi masa bayanai da matakan da suka dace a dauka.

“ An kuma umurci duk hafsoshin tsaron das u tabbatar da sun dauki matakai ba wai bincike ba har ma da daukar matakan tabbatar da an shawo kan matsalar sake faruwar harin nan gaba.

“Munci nasarar wannan taro kuma taron ya amince daukar kwararan matakai na tabbatar da irin wannan harin bai sake faruwa ba har abada.”

Dingyadi ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zasu gudanar da binciken kwakwaf kuma suna bukatar hadin kan aluma akan hakan domin yaki da duk assured Nigerians of a full scale investigation into the attack, as he solicited for their support in fighting all forms of criminality.

 

Ladan Nasidi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *