Ranar Ma’aikata: Shugaban PDP Ya Nema Ingantaccen Kunshin Jin Dadin Ma’aikata
Maimuna Kassim Tukur,Abuja.
Prince Dotun Babayemi, Shugaban a jam’iyyar PDP a Osun, ya yi kira da a inganta tsarin Jin dadin ma,aikata domin zaburar da su wajen yin aiki mai Kyau.
Babayemi ya yi wannan kiran ne a Osogbo a ranar Lahaina da ya gabata a wani sakon hadin Kai ga ma’aikatan Najeriya yayin da suke murnar zagayowar ranar ma’aikata ta bana.
Hakazalika ya yi kira ga gwamnati da ta Samar da tsars-tsare masu dorewa wadanda za su fi dacewa da rayuwa ga ma’aikatan Nijeriya kafin su yi ritaya.
Babayemi, wanda tsohon dan takarar gwamna ne a jam’iyyar PDP a jihar, ya zage damtse don Samun kyakkyawan yanayin aiki da zai Kara habaka tattalin arzikin kasa da kuma dakile kwalwa.
Ya bukaci gwamnati da ta Samar da mafita ta din-din-din don magance matsalar rashin biyan ‘yan fansho da garatuti na wadanda suka yi ritaya.
“Ya kamata gwamnati ta Samar da ingantattun Kayan aiki ga ma’aikata da za su wuce albashin wata-wata.
“Mugunta ne a bi bashin albashi,haka kuma rashin tsoron Allah kada a biya ‘yan fansho hakkokinsu daidai da lokacin da ya kamata.
Mugunta ce. “Ma’aikatanmu da wadanda suka yi ritaya sun cancanci a yi musu adalci ta tsarin ta hanyar tsars wa da kuma a zahiri, manufofi da shirye-shiryen da za su sa rayuwa ta kasance mai ma’ana da kuma dawwama a gare su yayin da bayan hidima,” in ji shi.
Babayemi ya bayyana cewa gaggauta biyan ma’aikatan da suka yi aiki da wadanda suka yi ritaya, zai kawo karshe hadama da cin hanci da rashawa da suka dabaibaye tsarin.
A cewarsa, idan da gaske gwamnati za ta iya ganin Jin dadin ma’aikata ta hanyar rashin mayar da hankali kan Karin albashi kadai, abubuwan da suka saba cin hanci da rashawa za su ragu.
Babayemi ya bukaci gwamnati da ta Kara kaimi ta fuskar inganta Jin dadin ma’aikata domin cire kwazo daga hannunsu.
Ya kuma yi kira ga ma’aikata a kowane mataki da su sake sadaukar da kansu don yin aiki domin kawo sauyi da ake bukata a dukkan sassan tattalin arzikin kasar
.
Leave a Reply