Gwamnatin Birtaniya ta taya Bola Tinubu da Kashim Shettima murnar rantsar da su a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa na Tarayyar Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babbar hukumar Burtaniya a Najeriya ta fitar.
A cikin wani sako da ya aikewa shugaba Tinubu, mai martaba Sarki Charles III ya jaddada aniyarsa na kulla alaka mai karfi da Najeriya.
Sarkin yace; “Ina so in mika maka sakon taya murna na murnar rantsar da ka a matsayin shugaban kasar tarayyar Najeriya tare da mika maka fatan alheri yayin da ka sauke nauyin da ke kan ofishinka.
“A matsayina na abokan hulɗar Commonwealth tare da zurfafa dangantaka, ina fatan haɓaka dangantaka mai ƙarfi tsakanin ƙasashenmu a lokacin shugabancin ku.”
Helen Grant OBE, wakiliyar Firayim Minista na musamman kan kasuwanci da ilimin ‘yan mata a Najeriya ta ce; “Abin da na sa a gaba shi ne karfafa huldar kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen biyu, don samun moriyar juna ga manyan kasashenmu biyu, kuma ina fatan yin aiki tare da sabuwar gwamnati don cimma wannan buri.
“A cikin wannan, ƙasar mahaifina, ina ƙaunar jama’arta sosai, kuma aikin da na yi na tabbatar da kowace yarinya ta sami ingantaccen ilimi na shekaru 12 shi ma zai ci gaba da kasancewa a saman ajandar Najeriya.”
A nasa bangaren, babban kwamishinan Burtaniya a Najeriya, Richard Montgomery ya ce; “Birtaniya na fatan yin aiki tare da sabuwar gwamnati yayin da muke tallafawa Najeriya mai wadata da juriya, da karfafa hadin gwiwarmu kan kasuwanci, ci gaba, da tsaro.”
Tawagar ta Burtaniya a wajen kaddamar da taron da aka yi a Abuja, ta samu jagorancin jakadiyar firaministan kasar kan harkokin kasuwanci a Najeriya, kuma jakadiyya ta musamman kan ilimin yara mata, Helen Grant OBE ‘yar majalisa da kuma babban kwamishinan Burtaniya a Najeriya, Dr. Richard Montgomery CMG.
Leave a Reply