An sauya dakarun rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) da aka girke a tafkin Chadi domin su kasance cikin taka-tsan-tsan da kuma tabbatar da tsaron fararen hula.
Kwamandan rundunar ta MNJTF, Manjo Janar Gold Chibuisi ne ya bayar da wannan umarni a wata ziyarar aiki da ya kai wa sojoji a Baga da Kauwa da kuma Bosso a sassa 3 da 4 na Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar soji, MNJTF Ndjemena- Chad, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce kwamandan ya tabbatar wa da sojojin cewa MNJTF ta dukufa wajen bayar da guummowar da ya dace domin gudanar da ayyukansu.
Haɗin gwiwa
Ya kuma karfafa gwiwar sojojin da su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro da shugabannin kananan hukumomi domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Janar Chibuisi ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar yankin da su yi taka tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga hukumomin tsaro.
Ya kuma kara da cewa, kungiyar ta MNJTF ta ci gaba da jajircewa wajen gudanar da aikin ta, kuma tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro za ta ci gaba da kare ‘yan kasa, da yaki da ta’addanci da kuma samar da zaman lafiya da tsaro a yankin tafkin Chadi.
Ƙarin Taimako
Kwamandan rundunar ya yabawa shugabannin yankin bisa goyon bayan da suke baiwa kungiyar MNJTF da ayyukan kasa baki daya.
Ziyarar da ya kai wa Hakimin yankin Bosso Arimi Shattima ya ba shi damar neman karin goyon baya daga shugabannin yankin da ‘yan kasa kan ayyukan MNJTF.
Kwamandan rundunar ya amince da cewa ya zama wajibi a hada kai domin yakar matsalolin da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin.
Leave a Reply