Take a fresh look at your lifestyle.

Gabon: Matakin mu ya zama dole- Jagoran Masu Juyin Mulki

Maimuna Kassim Tukur,Abuja.

0 188

 

Da yake magana bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban rikon kwarya na Gabon, Janar Brice Nguema ya kare kwace mulki a makon da ya gabata, yana mai cewa hakan na nuna kishin kasa ne.

 

 

Ya ambato tsohon shugaban mulkin soja na Ghana, kuma daga baya zababben shugaban kasa, Jerry John Rawlings, yana mai cewa: “Lokacin da shugabanni suka lalata kasa, to dole ne sojoji su mayar musu da mutuncinsu da ‘yancinsu.

 

 

“A cikin wannan ruhi ne mu sojojin tsaro muka dauki nauyinsu ta hanyar kin amincewa da tsarin zabe na son zuciya.”

 

 

 

Maimuna Kassim Tukur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *