Wata kungiya mai zaman kanta dake fafutukar yaki da jahilci da kuma tallafawa ayyukan ilimi mai suna NOGALSS a takaice ta tallafa wa ‘yan mata da mata sama da 10,000 da ba sa zuwa makaranta a fadin jihohi uku na Najeriya.
Kungiyar a cewar shugabanta Kwamared Noah Emmanuel na da burin isa dukkanin jahohi 36 na Najeriya da kuma Abuja, babban birnin tarayyar kasar, a wani gagarumin yunkuri na kawar da jahilci da bunkasa tattalin arziki da zamantakewa mai dorewa.
A yayin gabatar da takardun kama aiki ga sabbin mambobin kwamitin amaintattu na kungiyar ta NOGALSS wanda ya gudana ranar alhamis din nan a Abuja, Kwamared Noah Emmanuel ya bayyana cewa mata 4500 da suka ci gajiyar tallafin sun fito ne daga jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, dubu 3,000 daga jihar Ebonyi a kudu maso gabas da kuma 2,500 daga Abuja babban birnin kasar.
NOGALSS, wacce ke zama a matsayin uwar kungiyoyi masu zaman kansu, da kungiyoyin sa kai da ke gudanar da ayyukan tattafawa ilimin zamani na manya a Najeriya, tana yunƙurin samar da ingantaccen ilimi ga ‘yan mata da mata da ba sa zuwa makaranta.
Kwamared Emmanuel ya jaddada muhimmiyar rawar da kungiyar ke takawa wajen rajin yaki da jahilci da tsara manufofi, da aiwatar da gyare-gyare tun daga tushe, da samar da hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki.
Manufar kungiyar a cewar shugaban ita ce tabbatar da cewa al’ummar da ke fuskantar tarnaki a fannin ilimi da suka hada da yaran da ba su zuwa makaranta, da manya masu koyan karatu, da mata da sauran wadanda aka mayar saniyar ware, sun samu damar yin karatu mai inganci da ilimi.
A nasa jawabin Ambasada Lawal Saulawa, daya daga cikin amintattun kungiyar, ya yi kira ga gwamnati, da ‘yan siyasa, da sauran masu ruwa da tsaki, musamman a jihohin da suke fama da karancin mutanen da basu samu damar samun ilimi ba, da su tallafa wa NOGALSS domin cimma burin da ta ke muradi.
Abdullarim Rabiu
Leave a Reply