Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta ce nan da ‘yan makwanni za a fara kashi na biyu na yashe kogin Asa, domin kara zage damtse wajen dakile ambaliyar ruwa a Kwara.
Babban Sakatare na Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya Mista Shehu Ibrahim, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Ilorin, yayin wata ziyarar duba kogin Asa.
Gwamnatin jihar dai ta baiwa ma’aikatar tabbacin cewa za a sanya ido a kan wadanda ke zaune a kusa da kogin tare da hana su zubar da shara a tashar ruwa.
“Bayan da aka kwashe, tare da tarwatsa kogin, mutane na ci gaba da zubar da shara a cikin kogin.
“Wannan wani abu ne da ya kamata mu yi da gwamnatin jihar domin dakile ayyukan zubar da shara a cikin kogi da kuma cimma burinmu,” inji shi.
Ya kuma ce, kashi na biyu na aikin zai samar da matakan kariya da za su hana jama’a zubar da shara a kogin.
Har ila yau, Mista Bello El-Rufai, dan kwangilar da ke kula da aikin, ya ce aikin ya rage yawan ambaliya a jihar zuwa mafi karanci.
A cewar El-Rufai, a shekarar 2022, ba a samu rahoton ambaliyar ruwa a kewayen al’ummomin da ake gudanar da aikin ba.
Dan kwangilar ya ce, aikin nasu ya samu tsaiko sakamakon ruwan sama da ya kawo cikas ga aikin ginin daga watan Agusta zuwa Disamba.
“Lokacin da aka bayar na gudanar da aikin watanni 18 ne, amma an kara wa’adin watanni uku domin mu samu damar kammala ayyukanmu,” in ji El-Rufai.
Leave a Reply