Ɗan takara shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaɗa ƙuri’ar sa a mazaɓarsa da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano.
Kwankwaso ya fito ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe, inda ya kaɗa ƙuri’ar tasa.
Tsohon gwamnan jihar Kanon na ɗaya daga cikin ƴan takarar shugabancin ƙasa da ake ganin za su taka rawar gani a zaɓen na 2023.
Leave a Reply