Dan takarar shugabancin Najeriya na Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya kaɗa ƙuri’a a mazaɓar shi ta Awolowo da ke Falomo a Jihar Legas.
Da misalin ƙarfe 9:30 na safe ne dan takarar ya isa inda zai ƙaɗa kuri’ar tasa tare da mai ɗakinsa Oluremi Tinubu.
An samu jinkiri gabanin fara kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓen, sai dai daga baya zaɓen ya kankama. Akwai mutum aƙalla 832 da suka yi rajistarsu a wannan rumfar zaɓe.
Yayin da harkokin zaɓe ke ci gaba da gudana a wasu sassan Najeriya lami lafiya, wasu ɓangarorin suna fama da matsaloli da dama.
Kama daga rashin isar jami’an INEC a kan lokaci zuwa na rashin tsaro kamar a abin da ya faru a jihar Gombe.
A Jihar Maidugurin kuma akwai matsalar na’urarar tantance masu kaɗa ƙuri’a ita ce ta ƙi aiki yadda ya kamata.
Kazalika ana fuskantar rashin fitowar masu zaɓe a jihar.
Leave a Reply