Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamna Ishaku Ya Yi Kira Da A Tsawaita Lokacin Zabe A Jihar Taraba

0 155

Gwamnan jihar Taraba kuma dan takarar kujerar Sanatan Kudancin Taraba a karkashin jam’iyyar PDP, Darius Ishaku ya yi kira da a tsawaita lokacin kada kuri’a a jihar sakamakon rashin isar kayayyakin zabe a wasu sassan jihar.

Gwamna Ishaku wanda ya kada kuri’a a sashin zaben sa mai lamba PU 004 da ke Takum da misalin karfe 12:20 na rana ya roki hukumar zabe mai zaman kanta da ta tsawaita lokacin kada kuri’a a Taraba domin baiwa masu kada kuri’a a yankunan da kayan zabe suka isa a makare don yin amfani da katin zabe.

Ko da yake ya ce lokaci ya yi da za a tantance fasahar Biomodal Accreditation System (BVAS) da INEC ta tura, ya bayyana fatan jam’iyyarsa ta PDP za ta lashe zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a mazabarsa.

“Mun samu cikas game da rabon kayan zabe kuma an daidaita shi a makare. Yawancin yankunan sun karbi kayan zaben su a makare kuma ina so in yi kira ga INEC da ta kara lokacin zabe fiye da karfe biyu na rana,” inji shi.

An bayyana bacewar sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya mai lamba ECE8 a garin Takum, lamarin da ya tilastawa jami’an tsaro kirawo dukkan motocin da suka tashi zuwa unguwanni daban-daban na karamar hukumar Takum da su koma Takum a daren jiya domin tantance sakamakon da ya bata.

Kansila mai wakiltar Chanchanji Ward Hon. James Ugo wanda ya raka kayan zaben ya koma Takum da misalin karfe 11:45 na safe ya ce daga baya an gano takardar sakamakon zaben a kayayyakin zaben gundumar Dutse. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, Usman Abdullahi ya tabbatar da batan sakamakon zaben amma ya ce an warware matsalar.

“An bayyana bacewar takardar sakamakon zaben kuma an tsare jami’in zaben a gidan yari, amma daga baya an gano takardar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *