Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Bauchi Ya Kada Kuri’a Kuma Ya Yabi INEC Kan BVAS

0 147

Gwamnan jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya Sen Bala Mohammed ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC kan amfani da tsarin tantance masu kada kuri’a BVAS wajen gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Gwamnan ya yi wannan yabon ne bayan ya kada kuri’arsa a rumfar zabe mai lamba 008 Bakin Dutse, makarantar firamare ta Model ta Yelwan Duguri a karamar hukumar Alkaleri.

Gwamna Bala ya yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta tsawaita aiki da gaskiya da aka nuna a zabukan gwamnoni da na majalisun Jihohi domin karfafa nasarar da aka samu.

Da yake yiwa ‘yan jarida jawabi bayan kada kuri’a, Gwamnan ya yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali tare da yabawa al’ummar jihar bisa dimbin fitowar jama’a a garinsu da suka yi hakuri su gudanar da zaben.

Don haka Gwamnan ya bayyana fatan ‘yan takarar PDP za su yi nasara. Muryar Najeriya ta tattaro cewa Gwamnan da uwargidansa Hajiya A’isha Bala Mohammed ne suka kada kuri’unsu da misalin karfe 10:30 na safe bayan sun samu nasarar tantancewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *