Take a fresh look at your lifestyle.

PDP Ta Lashe Kujerar Sanatan Kaduna Ta Arewa

0 205

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Alhaji Khalid Ibrahim-Mustapha na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Kaduna ta Arewa.

Farfesa Saleh Ado na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, jami’in zabe na INEC ne ya bayyana sakamakon zaben a Zariya ranar Litinin.

A cewarsa, jam’iyyun siyasa 12 ne suka taka rawar gani a zaben. Ado ya ce Khalid-Mustapha ya samu kuri’u 250,026 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Sanata mai ci, Kwari Suleiman Abdu na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 190,008.

Ya ce Usman Bawa na NNPP ya samu kuri’u 28,511 ya zo na uku, yayin da Sidi Ibrahim Bamalli na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 28,418. Jami’in zaben ya kuma ce Ahmed Wakili na jam’iyyar PRP ya samu kuri’u 3,453; Abdullahi Suleiman na ADC mai 3,678 da Hassan Muktari na jam’iyyar ZLP da kuri’u 582.

“Khalid Ibrahim Mustapha na jam’iyyar PDP bayan ya cika sharuddan doka an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kuma aka dawo zabe,” in ji Ado.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *