Take a fresh look at your lifestyle.

Jam’iyyar APC Ta Lashe Kujerar Majalisar Tarayya Ta Toro A Bauchi

0 207

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Mista Ismail Dabo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar tarayya ta Toro a jihar Bauchi.

Jami’in Tantance Masu Kada Kuri’a na INEC, Mista Harami Adamu ne ya sanar da sakamakon zaben a ranar Litinin a cibiyar tattara sakamakon zaben da ke karamar hukumar Toro a jihar.

Ya ce Dabo ya samu kuri’u 46,691 inda ya doke abokin takararsa Isa Tilde na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 26,737. Haka kuma, Isa Kufai na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya samu kuri’u 13,333.

“Bayan cika sharuddan doka, Ismail Dabo na jam’iyyar APC an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kuma aka zabe shi a matsayin mamba mai wakiltar mazabar tarayya ta Toro a babban zaben 2023,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *