Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana Mista Habib Mustafa na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar majalisar dattawa ta Jigawa ta tsakiya.
Jami’in zabe na INEC, Farfesa Usman Haruna, wanda ya bayyana sakamakon zaben a ranar Litinin a Dutse, ya ce Mustafa ya samu kuri’u 153,731 inda ya zama wanda ya yi nasara.
Haruna ya ce Sanata Sabo Nakudu na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 134,802 inda ya zo na biyu.
Ya ce Mista Musa Bako na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya samu kuri’u 18,662, yayin da Mista Musa Abdullahi na ADC ya samu kuri’u 620.
Ya ce Hindatu Ibrahim ta NRM ta samu kuri’u 462, yayin da Gambo Bala Amina na SDP ya samu kuri’u 292.
Idan dai za a iya tunawa, Nakudu, Sanata mai ci shi ma dan majalisar wakilai ne na wa’adi biyu.
Leave a Reply