A ranar Litinin ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa INEC ta bayyana Hamisu Chidari, Kakakin Majalisar Dokokin jihar Kano a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Danbatta/Makoda.
Farfesa Haruna Musa na Jami’ar Bayero Kano (BUK), jami’in zaben ya bayyana Chidari na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar wakilai da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu bayan ya samu kuri’u 30,346.
Musa ya ce Chidari ya doke abokin takararsa na kusa, Badamasi Ayuba na NNPP, wanda ya samu kuri’u 24,792.
Hakazalika, INEC ta bayyana Abdulmumi Kofa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Kiru/Bebeji na jihar.
Jami’in kula da zaben Farfesa Sale Kumurya na BUK ne ya sanar da sakamakon zaben a Bebeji ranar Litinin. Kumurya ya ce Kofa ya samu kuri’u 40,463 inda ya doke abokin hamayyarsa Sunusi Saidu Kiru na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 34,798.
Bugu da kari, hukumar ta bayyana Sani Bala na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar tarayya ta Kunchi/Tsanyawa a jihar.
Farfesa F. Abdullahi na BUK, jami’in zaben ne ya bayyana sakamakon zaben a karamar hukumar Tsanyawa a ranar Litinin. Abdullahi ya ce Bala ya samu kuri’u 25,000, yayin da Safiyanu Mohammed na NNPP ya samu kuri’u 21,648.
Kazalika, Farfesa Sani Ibrahim na BUK, jami’in zaben mazabar Minjibir/Ungogo na tarayya, ya ayyana Adamu Sani na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar bayan ya samu kuri’u 49,274. Ibrahim ya ce Sani ya doke Marau Sani Nas na APC wanda ya samu kuri’u 16,629.
Leave a Reply