Sanata Abba Moro na jam’iyyar PDP ya yi nasarar lashe zaben Sanatan Benue ta Kudu a jihar Benue.
Jami’in zabe na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) mai wakiltar mazabar Benuwe ta kudu a Otukpo a jihar Benue a arewa ta tsakiyar Najeriya, Robert Ter, wanda ya bayyana haka a wurin tattara sakamakon zaben ya ce Sanata Abba ya samu kuri’u 76,459 inda ya doke babban abokin hamayyarsa Daniel Onjeh na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya samu kuri’u 59,959.
Da yake mayar da martani ga nasarar da ya samu, Sanata Morro ya ce “Na ji dadi da farin ciki kuma na ce tsarki ya tabbata ga Allah. Na sadaukar da wannan nasara ga Allah Madaukakin Sarki da Ya sa hakan ya yiwu ba tare da wata matsala ba.”
Daga karshe ya mika godiyarsa ga al’ummar mazabar majalisar dattijai inda ya ce, “Ga al’ummar mazabar zone C, ‘yan uwana na Idoma, ina so in gode muku. Na sadaukar da wannan nasara bayan Allah ga al’ummar mazabar Benuwe ta Kudu.”
Sanata Morro ya jaddada kudirin sa ga al’ummar Idoma land inda ya bada tabbacin cika alkawuran yakin neman zabe da kuma bayyana ra’ayoyinsu a majalisar dattawa ta 10.
“Abin da suka nuna shi ne sun cika alkawuran da suka dauka na zabe ni na koma Majalisar Dattawa kuma in zama masu fada a ji kuma na yi alkawarin zan ci gaba da zama masu fada a ji, zan ci gaba da yi musu hidima, zan ci gaba da fafutukan su,” in ji shi.
Don haka ya yi kira ga abokin hamayyarsa da su zo su yi wa mutanen Idoma hidima. Abba Moro tsohon mai kula da harkokin ilimi ne a Najeriya, kuma dan siyasa kuma tsohon ministan harkokin cikin gida na tarayya.
Sauran jam’iyyu sun yi nasara kamar haka;
AD – 828
ADP – 456
APC – 59,959
APGA – 2,361
LP – 40,194
NNPP – 1,414
PDP – 76,459
PRP – 264
SDP – 811
ZLP – 706
Leave a Reply