Mutane da dama ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan wani kazamin fashewar danyen mai a yankin Rumuekpe da ke karamar hukumar Emuoha a jihar Ribas a kudancin Najeriya.
Lamarin da ya faru da sanyin safiyar Juma’a ana kyautata zaton masu sana’ar tace danyen mai da aka sata ba bisa ka’ida ba da ke aiki a bututun Neja Delta a yankin.
Fashewar ta yi sanadiyyar asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira.
A halin da ake ciki, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni jami’in ‘yan sandan shiyya na kan gaba a lamarin.
Leave a Reply