Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka (AU), Moussa Mahamat ya taya zababben shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
An buga sakon taya murnan a shafin Twitter na AU a yammacin Juma’a, 3 ga Maris, 2023.
Shugaban ya yabawa ‘yan Najeriya kan yadda suka nuna jajircewa wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya ta hanyar jefa kuri’unsu ga shugabannin da suke so.
Don haka ya bukaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda, ya kuma kara da yin kira da a bi duk wani rikici ko korafe ta hanyar tsarin shari’a, kamar yadda doka ta tanada.
“Shugaban ya nuna matukar godiyarsa ga H.E. Uhuru Kenyatta, tsohon shugaban kasar Kenya bisa fitaccen shugabancinsa a matsayinsa na shugaban tawagar Tarayyar Afirka a Tarayyar Najeriya.
Shugaban ya kuma mika godiyarsa ga kungiyar ECOWAS da sauran abokan huldar hadin gwiwa da suka yi wajen ganin an gudanar da zabe cikin lumana a Najeriya.
“Shugabar ta sake sabunta kudurin kungiyar Tarayyar Afirka na tallafa wa ‘yan uwantaka ta Tarayyar Najeriya a yunkurinta na zurfafa dimokaradiyya, kyakkyawan shugabanci, da ci gaba mai dorewa da tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a kasar.”
Leave a Reply