Take a fresh look at your lifestyle.

Zaben Gwamnoni: Zababben Shugaban Kasa Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Yi Zabe Lami Lafiya

0 131

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya kada kuri’arsa a rumfar zabensa da ke Alausa a Ikeja, jihar Legas, a Kudu maso yammacin Najeriya.

 

Tinubu ya kada kuri’arsa ne tare da matarsa, Oluremi.

 

Zababben shugaban kasar ya yaba da yadda aka gudanar da zaben tare da karfafa gwiwar mazauna yankin da su kasance cikin lumana a duk lokacin gudanar da zaben.

Yace; “Na bi sahun sauran ’yan Najeriya wajen gudanar da ayyukana na jama’a a zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da ke gudana.

 

“Ina ƙarfafa ku duka ku fita ku yi zabe cikin lumana.”

Jami’an ma’aikatar tsaron kasar sun isa rumfar zabe ta Tinubu domin samar da tsaro a wani bangare na aikinsu ga zababben shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *