Jama’a sun fito kwansu da kwarkwata a sassan jihar Legas ta Kudu maso yammacin Najeriya domin kada kuri’a a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki.
A rumfar zabe mai lamba 057 Okota Ward Oshodi Isolo dake wajen birnin Legas, hukumar zabe mai zaman kanta, jami’an INEC sun isa wurin da karfe 10:25 na safe agogon kasar.
An fara tantance masu kada kuri’a da kada kuri’a nan take. Na’urar tantance masu kada kuri’a ta Bimodal BVAS tana aiki daidai kuma ana gudanar da atisayen cikin lumana.
Babu wani jami’in tsaro a kasa wajen ja na’urar 057, amma suna can a wasu rumfunan zabe, domin tabbatar da an gudanar da zaben cikin lumana.
Leave a Reply