Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Buhari Ya Yi Allah-Wadai Da Kashe-Kashen Da Ake Yi A Jihar Benue

0 347

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi a jihar Benuwe.

An kashe mutane goma a unguwar Umogidi da ke Entekpa-Adoka a karamar hukumar Otukpo a jihar.

Don haka Shugaba Buhari yana kira da a yi duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen tashe-tashen hankula

A cikin wani sako da ya aike, shugaban ya yi Allah wadai da amfani da ta’addanci a matsayin wani makami a cikin rikice-rikicen kabilanci, inda ya bukaci da a gano maharan tare da magance su cikin gaggawa a karkashin doka.

Ya mika alhininsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin, ya kuma umurci jami’an sirri, ‘yan sanda da kwamandojin soji da su kara sanya ido a kowane fanni da kuma gaggauta duba jami’an tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.

Shugaban ya ce; “Tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da iyalan wadanda aka kashe. Al’ummar kasa baki daya sun tsaya tsayin daka wajen yakar dakarun ta’addanci da miyagun ayyuka.”

Aisha Yahaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *