Take a fresh look at your lifestyle.

Gbajabiamila Yayi Kira Da Zaman Lafiya A Lokacin Gudanar Da Bikin Ista

0 229

Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya taya mabiya addinin kirista a fadin kasar murnar bikin Ista na bana.

 

 

Gbajabiamila ya ce wannan lokaci yana da matukar muhimmanci kuma yana kira da a yi tunani a hankali a tsakanin Kiristoci domin bikin tashin Yesu Almasihu daga matattu.

 

Kakakin majalisar, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Lanre Lasisi ya fitar, ya yi kira da a zauna lafiya a tsakanin ‘yan Nijeriya a yanzu da kuma ko da yaushe.

 

Kakakin majalisar Gbajabiamila ya bukaci ‘yan kasar musamman mabiya addinin Kirista da su yi amfani da wannan lokacin wajen yin addu’o’in samun sauki a ranar 29 ga watan Mayu.

 

Ya kuma yi kira da a yi addu’a ga gwamnatin zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, da kuma sauran shugabannin kasar nan.

 

Gbajabiamila ya yi wa daukacin al’ummar Kiristocin kasar fatan murnar bikin Ista.

 

 

Aisha Yahaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *