Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar ICPC Ta Kama Wasu Mutane 9 Da Ake Zargi Da Sayan Kuri’u A Ondo Da Osun

0 156

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta kama wasu mutane 9 da suke sayen kuri’u a jihohin Osun da Ondo dake kudu maso yammacin Najeriya.

Hukumar ta kuma kama masu aikata laifuka a jihohin Borno, Akwa Ibom, da Sokoto.

Hukumar ta ICPC ta bayyana a shafinta na Twitter cewa, an damke masu laifin ne a yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar.

“Ofishin ICPC na jihar Osun sun kama masu sayen kuri’u hudu, ofishin jihar Sokoto kuma mutum biyu sun kama, yayin da ofishin Ondo, Akwa Ibom da kuma Borno na hukumar yaki da cin hanci da rashawa suka kama kowannensu,” hukumar ta wallafa a shafinta na twitter. .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *